Hukumomin lafiya na duniya sun amince da allurar Ebola a Congo

Wasu da ke karbar allurar magance cutar ta Ebola a garin Goma na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo
Wasu da ke karbar allurar magance cutar ta Ebola a garin Goma na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo REUTERS/Djaffer Sabiti

A karon farko hukumomin da ke kula da magunguna na Turai sun amince da sabuwar allurar magance cutar Ebola wadda aka fara amfani da ita a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, matakin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana da gagarumin ci gaba da zai kawo karshen rasa rayukan da ake fuskanta sanadiyyar cutar mai matukar hadari.

Talla

Allurar wadda wani fitaccen masanin magunguna ba’Amurke ya samar, tuni aka fara amfani da ita don bayar da taimakon gaggawa ga jam’a a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo amma ba tare da sahalewar hukumomin lafiya na Turai ba.

Allurar wadda aka samar da ita karkashin kamfanin harhada magunguna na Merck & Co sai da ta samu sahalewa daga mahukuntan lafiya na kasar ta Amurka kafin sahale fara amfani da ita tun a wancan lokaci.

A cewar Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanim kawo yanzu allurer ta ceci tarin rayuka daga salwanta a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da ke fuskantar annobar cutar karo na 10.

Kawo yanzu dai mutane dubu 2 da dari 1 suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar ta Ebola tun bayan sake barkewarta a bara, yayinda a jumulla ta hallaka rayuka dubu 11 da dari 3 a yammacin Afrika baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.