Isa ga babban shafi
Nijar

Ambaliyar ruwa ta raba mutane dubu 23 da muhallansu a Nijar

Yadda ambaliyar ruwa ta yiwa jama'a banna.
Yadda ambaliyar ruwa ta yiwa jama'a banna. AFP /Mission Fellowship
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Rahotanni daga yankin kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar sun bayyana yadda ambaliyar ruwa da tilastawa mutane dubu 23 tserewa daga muhallansu wanda ke matsayin wani sabon kalubale ga kasar da ke tsananin bukatar agajin jinkai.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa mamakon ruwan da aka fuskanta cikin watanni ukun baya-bayan nan ne ya tumbatsa tekunan Komadougou na Yobe da ke tafiya ta cikin tafkin Chadi wanda shi kuma ya haifar da ambaliyar ruwa a kananun tafkuna da rafuna da ke sassa daban-daban na Najeriya da Nijar.

Wata kididdiga ta nuna yadda ruwa ya cinye wasu kananun kauyuka biyu da ke jihar Diffa wanda ya tilastawa magidanta dubu 2 da dari 5 ficewa don neman mafaka.

Kididdigar ta nuna cewa yanzu haka akwai sauran iyalai dari 4 da ke rayuwa a bukkoki cikin kauyukan wadanda kuma ke fuskantar ambaliya a kowanne lokaci.

Baya ga mutane da ambaliyar ruwan ta yiwa illa, ruwan ya kuma lallata tarin amfanin gona baga ga ruguje galibin gidajen dukkanin kauyukan da ke gab da tafkunan.

Daga watan Yuni zuwa Satumban jiya dai, mutane 57 ambaliyar ruwa ta hallaka a Jamhuriyyar Nijar yayinda adadin mutum dubu 130 suka rasa matsugunansu a sassa daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.