Tattalin arzikin Afrika na Tafiyar hawainiya- IMF

Kristalina Georgieva shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF.
Kristalina Georgieva shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF. Yasuyoshi CHIBA / AFP

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce bashin da ake bin kasaashen Afirka da ke Yankin kudu da sahara na daidaituwa, amma tattalin arzikin Yankin na fuskantar matsaloli sakamakon tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.

Talla

Abebe Aemro Selassie, Daraktan Asusun na IMF sashen da ke kula da Afirka ya ce basussukan da ake bin kasashen ya tsaya a matsayin kashi 55, kuma ana iya samun cigaba idan kasashen da ke Yankin suka aiwatar da kasafin kudaden su bisa ka’ida.

IMF ya bayyana kasashe 7 da suka hada da Eritrea da Gambia da Mozambique da Congo da Sao Tome da Sudan ta kudu da kuma Zimbabwe a matsayin masu fama da dimbin bashi, yayin da wasu Karin kasashe 9 cikin su harda Habasha da Kamaru da Ghana na fuskantar barazanar basuka masu yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.