Afrika da Rasha na cinikayyar da ta haura darajar biliyan 20 a shekara

Wasu shugabannin Afrika yayin taron da ke gudana tsakaninsu da Rasha.
Wasu shugabannin Afrika yayin taron da ke gudana tsakaninsu da Rasha. RFI/Hausa

Shugaban Rasha Vladimir Putin da ke jagorantar taron yini biyu da takwarorinsa na Afirka a garin Sochi, ya ce a cikin shekaru 5 kasar za ta rubanya alakar da ke tsakaninta da nahiyar, a daidai lokacin da bayanai ke cewa alakar da ke tsakanin bangarorin biyu ta haura ta dala bilyan 20 a shekara.

Talla

Yayin jawabin farko na bude taron a birnin Sochi, shugaba Putin ya ce yanzu haka, Rasha ta na shigar da kayayyakin abinci kasuwannin nahiyar Afrika, da darajarsu ta kai dala biliyan 25 a duk shekara, adadin da ya zarta cinikin makaman da Rashar ke yi da kasashen na Afrika.

Gwamman shugabanni da wakilan kasashen Afrika yanzu haka ke halartar taron karfafa alaka da Rasha, wanda shi ne irinsa na farko, dake zama yunkurin kasar wajen yin tasiri a nahiyar Afrikan musamman ta fuskokin tattalin arziki da kuma tsaro, kamar yadda wasu kasashen Yammacin Turai da kuma China suka yi.

Ana sa ran wakilai sama da dubu 3 dake halartar taron na kwanaki 2, za su tattauna gami da kulla yarjeniyoyi kan batutuwan fasahar inganta makamashin nukiliya, da kuma karfafa hakar ma’adanai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.