Isa ga babban shafi

Rasha za ta karfafa cinikayyar makamai da Afrika

Wasu shugabannin Afrika karkashin jagorancin shugaban Rasha Vladimir Putin a Sochi.
Wasu shugabannin Afrika karkashin jagorancin shugaban Rasha Vladimir Putin a Sochi. RFI/Hausa
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Kasar Rasha ta bayyana aniyar karfafa cinikayyar makamai da jiragen Shalikwafta tsakaninta da Nahiyar Afrika dai dai lokacin da shugaba Vladimir Putin ke karbar bakoncin taron kasashen Afrika irinsa na farko a birnin Sochi.

Talla

Sashen fitar da makamai na Rasha ya baje kolin wasu makamai sabbin kira samfurin Kalashnikov da ke sarrafa kansu ciki har da jiragen yaki baya ga manyan bindigu gaban shugabannin Afrika wadanda tuni gwamnatin Rasha ta fara kula yarjejeniyar sayar da makamai da wasunsu yayin taron da ke gudana tsakaninsu a birnin Sochi.

Taron wanda ya faro daga jiya Laraba zuwa yau Juma’a ya hado kan mahukunta da wakilan kasashen na Afrika wadanda suka tattauna batutuwan da suka shafi fasahar nukiliya baya ga batun albarkatun karkashin kasa da kuma noma, sai dai kebantacciyar tattauna ta fi karkata kan batun cinikayyar makamai tsakanin kasar ta Rasha da nahiyar.

Rasha dai na matsayin ja gaba ta fannin shigar da makamai nahiyar Afrika yayinda taron ke fatan bunkasa cinikayyar don fatattakar ayyukan ta’addancin da suka dabaibaye kasashen nahiyar.

A cewar Daraktan sashen fitar da makamai na Rasha Alexander Mikheev kasar za ta fadada mu’amalarta da Nahiyar Afrika musamman bayan wata ganawa da za ta shirya tsakaninta wakilan manyan kasashen nahiyar 15.

Yanzu haka dai Rasha na samun kashi 40 cikin dari na cinikin makamanta ne daga nahiyar ta Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.