Isa ga babban shafi
Nijar

Hama Amadou zai koma gida Nijar

Jagoran yan adawa jamhuriyar Nijar  Hama Amadou
Jagoran yan adawa jamhuriyar Nijar Hama Amadou RFI Hausa
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Hukumar zaben Nijar ta kaddamar da shirin yiwa yan kasar dake zaune waje rijista.A wasu kasashen kwamity dake da nauyin tafiyar da wadanan ayuka na fuskanatar matsalloli,yayinda bangaren yan adawa suka koka da irin yada hukumomin na Nijar suka mayar da su daya geffen.

Talla

A Cote D’ivoire, na’urorin da ake amfani da su domin yiwa jama’a rijista na fuskantar matsalloli kamar dai yada mai magana da sunan jam’iyyar adawa ta Lumana a kasar ta Cote D’Ivoire Elhaji Soumana Yakouba ya sheida mana.

A daya wajen Elh Soumana Yakouba ya yi amfani da wannan dama domin isar da ta’azziyar sa zuwa Shugaban Jam’iyyar Hama Amadou da Allah ya yiwa mahaifiyar sa rasuwa a Nijar.

Wasu bayanai na nuni da cewa yanzu haka wasu kasashe da suka hada da Faransa na kokarin shiga tsakani domin bai wa shugaban babbar jam’iyyar adawa a kasar Moden-Lumana Africa wato Hama Amadou damar komawa kasar, bayan da ya share dogon lokaci yana zaune a waje .

Yanayin siyasa a jamhuriyar Nijar na ci gaba da tayar da hankulan kungiyoyin farraren hula da wasu jam'iyyoyin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.