Isa ga babban shafi
Mali

'Yan bindiga sun sace malaman makaranta

Wasu sojojin kasar Mali.
Wasu sojojin kasar Mali. AFP/PHILIPPE DESMAZES
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton cewar masu ikirarin jihadi ne, sun sace malamai 6 a yankin tsakiya Mali, saboda yin magana da kuma koyar da dalibai cikin harshen Faransanci.

Talla

Wani shaidar gani da ido, ya ce kafin sace malaman, sai da ‘yan bindigar suka kona tarin litattafan dalibai a farfajiyar makarantar.

Harin na baya bayan nan ya zo ne bayan da wata kididdiga ta nuna cewar, sama da makarantu 900 aka rufe a sassan kasar Mali, sama da kashi 2 bisa 3 daga cikinsu kuma a yankin tsakiyar kasar, saboda matsalolin tsaron da suka hada da na ta’addanci da kuma rikicin kabilanci.

A shekarar 2012 matsalar tsaro ta girmama a Mali, bayan da mayakan masu ikirarin jihadi da suka yi wa kungiyar Al-Qaeda mubaya’a suka mamaye arewacin kasar, bayan da sojojin kasar suka gaza murkushe tawayen Azbinawa.

Sai dai a shekarar 2013 dakarun Faransa suka kawo dauki, inda suka yi nasarar kwace mafi akasarin yankunan da mayakan suka mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.