Isa ga babban shafi
Mali

Madugun 'yan tawaye ya bukaci rikidewar takwarorinsa zuwa siyasa

Jagoran tsaffin mayakan 'yan tawaye na kungiyar HCUA, Alghabass Ag Intalla da mukarrabansa, yayin tattaunawa da wakilan gwamnatin Mali a birnin Ouagadougou, na Burkina Faso. 10/6/2013.
Jagoran tsaffin mayakan 'yan tawaye na kungiyar HCUA, Alghabass Ag Intalla da mukarrabansa, yayin tattaunawa da wakilan gwamnatin Mali a birnin Ouagadougou, na Burkina Faso. 10/6/2013. AFP/AHMED OUOBA
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Daya daga cikin kungiyoyin ‘yan tawayen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya shekara ta 2015 a Mali (HCUA), ta ce tana goyon bayan dunkulewar tsaffin kungiyoyin ‘yan tawayen a matsayin jam’iyyar siyasa.

Talla

Jagoran kungiyar ‘yan tawayen Alghabass Ag Intalla, shi ne ya yi wannan tayi a lokacin da yake jagorantar taron kungiyarsa a garin Kidal, dake matsayin matattarar ‘yan tawayen tun bayan faduwar gwamnatin Amadou Toumani Toure.

Sai dai babu tabbas kan ko sauran kungiyoyin ‘yan tawayen da suka hada da CMA, MNLA, MAA za su amince da tayin na dunkulewa don kafa jam’iyyar siyasa ba.

A shekarar 2015, kungiyoyin ‘yan tawayen da suka kunshi tsaffin mayaka masu ikirarin jihadi na kungiyar Ansarudeen, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, inda suka yi watsi da akidarsu ta ‘yan aware, domin zaman lafiyar kasar Mali.

A karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar, za a sanya tsaffin ‘yan tawayen cikin rundunar sojin kasar ta Mali, da kuma baiwa yankin azbinawa dake arewacin kasar Karin damar amfana da kwaryakwaryar cin gashin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.