Tanzania

Magufuli na neman kashe aikin jarida a Tanzania

Shugaban Tanzania John Pombe Magufuli
Shugaban Tanzania John Pombe Magufuli REUTERS/Sadi Said

Kungiyoyin Amnesty International da Human Rights Watch sun ce, shugaban kasar Tanzania, John Magufuli na tirsasa wa kafofin yada labarai da kuma kungiyoyin fararen hula wajen hana su gudanar da ayyukansu.

Talla

Sanarwar da kungiyoyin suka fitar, ta  zargi shugaba Magufuli da kama 'yan jaridu yana daure su tare da shugabannin kungiyoyin fararen hula da kuma 'yan siaysar da ke adawa da manufofinsa.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da mulkin Magufuli ke cika shekaru 5 a watan gobe, yayin da ya yi kaurin sunan wajen hana jama’a fadin albarkacin bakinsu, wanda ya saba wa matsayin Tanzania kafin ya hau karagar mulki.

Roland Ebole, jami'in  bincike a Amnesty International ya ce, Tanzania na wuce gona da iri wajen take hakkin bil'adama, ganin irin tirsasawar da ake yi wa jama’a da kuma rufe kafofin yada labarai.

Ita kuwa Human Rights Watch ta bayyana rufe gidajen jaridu da katse mahawarar majalisa da ake nunawa ta kafar talabijin da kuma daure 'yan adawa a matsayin abin da ya zama ruwan dare a karkahin mulkin Magufuli.

Kungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda aka kama Erick Kabendera, aka tuhume shi da cin amanar kasa da kuma yadda Azory Gwanda ya bata a shekarar 2017 kuma har ya zuwa yanzu babu wanda ya ji duriyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.