Isa ga babban shafi
Afrika

Ambaliya ta tagayyara sama da mutane miliyan 1 a Afrika

Wani sashi na yankin Diffa a Jamhuriyar Nijar da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Wani sashi na yankin Diffa a Jamhuriyar Nijar da ambaliyar ruwa ta mamaye. UNOCHA
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

Kididdiga ta nuna cewar ambaliyar ruwa ta raba sama da mutane miliyan 1 da muhallansu a sassan kasashen Afrika da dama cikin wannan shekara ta 2019.

Talla

A bana dai wasu daga cikin kasashen nahiyar ta Afrika da suka fi fuskantar ambaliyar akwai, Habasha, Najeriya, Nijar, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sai kuma Somalia da Sudan ta Kudu.

A jerin kasashen da aka zayyano dai ambaliyar a bana ta fi shafar adadin mutane mafi yawa Sudan ta Kudu, inda a wannan wata na Oktoba Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 800 ne suka rasa muhallansu. A Habasha kuwa sama da mutane dubu 200 ambaliyar ta tagayyara, yayinda a Somalia adadin ya kai dubu 70.

Sai kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da sama da mutane dubu 6 suka rasa muhallansu a dalilin ambaliyar ruwa, duka cikin wannan wata na Oktoba.

A Najeriya kuwa rahoton da hukumomin kasar suka fitar ya nuna cewar ambaliyar ruwan ta soma munana cikin watan Agustan da ya gabata, inda a jihar Niger kadai hukumar bada agajin gaggawa ta ce kusan mutane dubu 42 suka rasa muhallansu, bayan da gidaje dubu 2 da 714 suka rushe.

A Adamawa kuwa kimanin kauyuka 40 dake kananan hukumomin jihar 7 ne ambaliyar ruwan ta mamaye. A kudancin Najeriya ma jihohin Legas da Ogun basu tsira daga Iftila’in ba.

A jamhuriyar Nijar, ofishin agajin jin kai na majalisar dinkin duniya y ace a farkon watan Oktoban da muke ciki kadai, ambaliyar ruwa ta tilastawa mutane dubu 23 tserewadaga muhallansu a yankin Diffa, saboda tumbatsar kogin Komadougou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.