Kamaru

Sama da mutane 40 sun halaka a dalilin zaftarewar kasa

Jami'an agaji da sauran jama'ar gari yayin aikin tonu wadanda zaftarewar kasa ta binne a garin Befusam dake yammacin kasar Kamaru. 29/10/2019.
Jami'an agaji da sauran jama'ar gari yayin aikin tonu wadanda zaftarewar kasa ta binne a garin Befusam dake yammacin kasar Kamaru. 29/10/2019. AP/Leclerc Tsakem

Akalla mutane 42 suka halaka a Kamaru sakamakon zaftarewar kasa a yankin Bafusam dake yammacin kasar.

Talla

Yanzu haka dai jami’an agaji na ci gaba da aikin ceto laluben gawarwaki da kuma wadanda suka yi sa’ar tsira da rayukansu.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar akwai fargabar karuwar adadin wadanda suka halaka a iftila’in zaftarewar kasar.

Habu Adam daya daga cikin mazaunan garin na Befusam da ambaliyar ta mamaye, ya ce gwamnati da hadin giwar jami’an agaji sun soma aikin tantace gidajen da ke fuskantar hadarin ambaliya, zaftarewar kasa ko kuma rushewa, domin fitar da mutane don gudun karuwar adadin wadanda iftila’in ya shafa.

Cikin watan Yulin shekarar 2018, mutane 5 suka rasa rayukansu a garin Limbe dake kudu maso gabashin kasar ta Kamaru, a dalilin zaftarewar kasar da ta biyo bayan ambaliyar ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.