Nijar

Sojojin Nijar 12 sun rasu a harin 'yan Boko Haram

Bayanai daga Jamhuriyr Nijar sun tabbatar da cewa dakarun kasar da dama ne suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai kan wani barikin soji da ke cikin jihar Diffa a kudu maso gabashin kasar.

Sojojin Nijar kusa da iyakar kasr da Najeriya
Sojojin Nijar kusa da iyakar kasr da Najeriya Reuters
Talla

Bayanai sun ce ‘yan bindiga masu tarin yawa ne suka afka wa barikin sojin garin Blabrine a cikin daren talatar zuwa wayewar garin yau laraba, inda suka dauki dogon lokaci suna musayar wuta da sojoji a wannan gari mai tazarar kilomita 40 daga N’guiguimi da ke jihar Diffa.

Majiyoyi sun ce adadin sojojin da suka kwanta dama zai kai 12 yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Wasu majiyoyi kuwa sun tabbatar da cewa, ko baya ga asarar rayukan, maharan sun kona motoci da makamai da dama a cikin wannan barik kafin a murkushe su. Har ila yau 'yan bindigar sun yi awun gaba da motoci da dama, to dai wata majiyar tsaro ta ce an kwato hudu daga cikin motocin.

Barikin sojin da ke Blabrine, na a wani yanki ne da ya jima yana fama da ayyukan Boko Haram kusa da tafkin Chadi, kuma harin na daren jiya, ya faru ne kwanaki 10 bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi awun gaba da magajin garin Kabalewa da kuma matarsa duk a wannan yanki na Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI