Faransa na neman kara zuba jari kasashen Afirka

Ministan kudin kasar Faransa Bruno Le Maire, wanda ya bayyana shirin kasar na zuba jari kasuwannin Afrika
Ministan kudin kasar Faransa Bruno Le Maire, wanda ya bayyana shirin kasar na zuba jari kasuwannin Afrika REUTERS/Gonzalo Fuentes

Ministan tattalin arzikin Faransa Bruno Le Maire, ya bukaci kara karfafa rawar da faransa ke takawa wajen zuba jari a nahiyar Afrika ta hanyar kara zaburar da kamfanonin faransa da su bazama zuwa zuba hannayen jari a nahiyar.

Talla

A cikin wani jawabi da ya gabatar ga taron tattalin arziki mai taken Ambition Africa, karo na biyu, da aka fara Laraban zuwa Alhamis a Bercy dake wajen birnin paris, ministan tattalin arzikin kasar Bruno Le Maire ya ce, Zuba jari a kamfanonin nahiyar Afrika ne babban kalu balen farko da ya kamata a fuskanta a kokarin da ake na bunkasa tattalin arzikin nahiyar.

Domin cimma wannan manufa, faransa na da muhimmiyar rawar da ya kamata ta taka :

A lokacin da yake bayyana alkawarin da shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya dauka yayin ziyarar sa kasar Burkina Faso shekaru biyu da suka gabata Le Maire, ya ce Faransa na bukatar ganin ta samar da wani dandali na masu zuba jari a nahiyar ta Afrika.

Dangane da wannan sabon tsari da ake yiwa lakabi da Choose Africa, da aka kaddamar a watan Maris din da ya gabata a Dakar babban birnin kasar Senegal, Faransa ta bayyana ware Euro biliyan biyu da rabi, wajen zuba jari a masana’antun nahiyar ta Afrika, kudaden da suka hada da tsabar kudi biliyan 1 na Euro da kuma wasu biliyan daya da rabi a matsayin bashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.