Amurka ta janye Kamaru daga cikin masu amfana da garabasar cinikaya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Amurka ta sanar da dakatar da garabasar da Kamaru ke amfana da ita daga cikin jerin kasashe da suka rataba hannu a yarjejeniyar kasuwanci da ake kira AgoaDaukar mataki na zuwa ne bayan da rahotani daga Amurka suka gano cewa Kamaru ta keta wasu daga cikin dokokin da kasashe suka cimma da kuma batutuwa da suka jibanci kare hakokin bil Adam.
Sanarwar da Amurka ta fitar a jiya alhamis na bayyana cewa matakin janye garabasar zuwa Kamaru daga Amurka zai soma aiki kama daga farkon watan janairu shekarar 2020.
Mai wakiltar cibiyar yan kasuwar Amurka J Mahoney ya jaddada aniyar hukumomin kasar sa na ci gaba da kawo na su gundunmuwa don taimakawa Kamaru a fanoni da suka jibanci diflomasiya da kuma hulda da sauren kasashen Duniya.
Jami’in ya bayyana farin cikin sa ganin rawar da Shugaban kasar Paul Biya ya taka tareda sallamar wasu daga cikin yan siyasa dake tsare da kuma shirya babban taron sassanta yan kasar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu