Najeriya-Afrika

An cafke wani fasto da ya daure mutane da sarka a cocinsa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya ba da umurnin rufe gidajen azabtarwa
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya ba da umurnin rufe gidajen azabtarwa AFP/SAUL LOEB

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wani fasto bisa zargin sa da hannu wajen daure wasu mutane da sarka a wani coci da aka mayar da shi sansanin azabtar da jama’a jihar Lagos da ke kudancin kasar.

Talla

‘Yan sandan sun ceto mutane 15 cikin mari a samamen da suka kai harabar cocin da aka tsare su.

Wasu bayanai na cewa, akwai wadanda suka shafe shekaru biyar suna shan azaba a wannan sansani.

A cewar ‘yan sandan, sun kai samamen ne biyo bayan tsaegunta musu da aka yi cewa wani fasto yana gana wa wasu azaba a wani sansani.

Samamen da ‘yan sanda suka kai harabar cocin faston a yankin Isheri Osun na jihar Legas ya kai ga cafke faston mai suna Sunday Joseph, wanda ya saka mutane 15 cikin mari.

Bugu da kari, an cafke wasu mutum 10 wanda ma’aikata ne a cocin, wadanda ke taimaka wa faston wajen gana wa mutanen azaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.