Turai

Kasashen Turai sun bijirewa dokokin kula da yan cin rani

Wasu daga cikin yan gudun hijara a Turai
Wasu daga cikin yan gudun hijara a Turai REUTERS/Antonio Parrinello

Wata Jami’an Kotun kungiyar Tarayar Turai ta sanar da cewa kasashen kungiyar uku da suka hada da Janhuriyar Czech, Hungary da Poland sun sabawa dokokin kungiyar saboda kin karban ‘yan gudun hijira a shekarar 2015.

Talla

A cewar kotun dai kin amincewa da tsarin karban ‘yan gudun hijiran kasashen uku sun karya dokokin kungiyar Tarayar Turai

Kasar Poland dai ta soki wannan suka da aka yi masu inda wani kakakin Gwamnatin ke cewa babban abin bukata shine samar da tsaro ga ‘yan gudun hijiran, saboda wai dukkan wani mataki da kasar za ta dauka da niyyar yin abinda zai dadadawa mutan Poland ne.

Ita ma dai Gwamnatin Firaminista Viktor Orban na Hungary ta soki sanarwan inda take cewa bata sauya matsayinta ba dangane da batun kin cusa mata ra’ayin karban ‘yan gudun hijira da ‘yan Cin-rani.

A shekara ta 2015 ne dai a lokacin da kasashen Turai ke fama da matsalolin kwararan ‘yan gudun hijira, mafi yawa daga Syria, Kungiyar Turai ta bullo da wani tsari na wucin gadi, don tsugunar da dimbin ‘yan gudun hijiran dake jibge, a Italia da Girka zuwa sauran kasashen kungiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI