Isa ga babban shafi
Afrika

Sarakunan Afrika sun baiwa Paul Biya lambar yabo

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya RFI/Capture d'écran
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Wata kungiyar sarakunan gargajiyar nahiyar Afrika da ta gudanar da wani taro a Jamhuriyar Benin,taron da ya samu halartar Shuwagabanin gargajiya da daga kasashen Afrika ya bukaci yan siyasar nahiyar su saka shuwagabanin gargajiya a cikin harakokin tafiyar da al’amuran mulki a nahiyar.

Talla

Har ila yau taron ya karama Shugaban kasar Kamaru Paul Biya kan kokarin da yake wajen sake samar da zaman lafiya a kasar ta Kamaru.

Shugaban wannan kungiya da ake kira Panafrican Council of Traditional and Customary Authorities PACTCA, Dada Awiyan Octave Sarkin Dahe a jamhuriyar Benin ya bayyana Shugaban Kamaru Paul Biya a matsayin mutumen dake da hangen nesa.

Shugaban kungiyar ya na mai fatan Shugabanin Afrika za su yi koyi tareda saka Sarakunan gargajiya a lamuran yau da na kullum a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.