Mali-Faransa

Sojan Faransa halaka bayan taka nakiyar da IS ta binne

Sojan Faransa a kasar Mali
Sojan Faransa a kasar Mali RFI / Olivier Fourt

Ministan rundunonin sojan Faransa, uwargida Florence Parly ce ta bada sanarwar mutuwar dakaren na Faransa a wannan asabar, 2 ga watan Nuwamba.

Talla

Uwargida Parly ta bayyana shirinta na kai ziyarar aiki a kasar ta Mali nan gaba, ziyarar da za ta bata damar tattaunawa da hukumomin kasar, inda ake sa ran su tabo batutuwa da dama musamman ta fannin da ya shafi tsaro.

Sojan da ya gamu da ajalinsa Ronan Pointeau, daya ne daga cikin sojojin da Faransa ta aika a kasar ta Mali .

Tuni dai Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan mamacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI