Faransa-Afrika

Kyautar Ghislaine Dupont da Claude Verlon daga RFI

: Marie-Christine Saragosse da France Media Monde,tareda mutanen da suka lashe kyautar Ghislaine da Claude taraeda Cécile Mégie, Shugabar RFI
: Marie-Christine Saragosse da France Media Monde,tareda mutanen da suka lashe kyautar Ghislaine da Claude taraeda Cécile Mégie, Shugabar RFI RFI

Gidan rediyon Faransa Rfi a ranar biyu ga wanan watan da muke cikin sa ya bayar da kyautar nan da aka da sunan yan jarida nan Ghislaine Dupont da Claude Verlon da wasu yan bindiga suka kashe a garin Kidal dake arewacin Mali shekaru shida da suka gabata.

Talla

A wanan karon daga cikin ma’aikatan kaffafen yada labarai na Jamhuriyar Demokkuradiyar Congo 200 ,guda 20 ne yanzu haka za su amfana da wannan garabasa.

Banda haka biyu daga cikin su da suka nuna hazaka a wannan aiki da suka hada da Myriam Iragi Maroy mai shekaru 30 da kuma ke aiki a wani gidan rediyo mai suna Radio Top Congo a Kinshasa da mai gyaran sautuka ko injiniya Vital Mugisho mai shekaru 26 ne yanzu haka za su je Paris inda za a basu horo dangane da dabarun aikin jarida a watan Fabrairu shekarar 2020.

Shugabanin Rediyon Faransa da suka hada Marie Christine Saragosse daga France Media Monde da Cecile Megie ne suka bayar da wadanan kyaututuka a Kinshasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.