Mali

IS ta dauki alhakin halaka sojojin Mali 49

Wasu sojojin Mali a gefen wani gini da mota da suka kone a birnin Gao. 13/11/2018.
Wasu sojojin Mali a gefen wani gini da mota da suka kone a birnin Gao. 13/11/2018. AFP

Kungiyar IS ta dauki alhakin kashe sojojin Mali 49, a farmakin da ta kaiwa sansaninsu a Indelimane, dake yankin Menaka mai iyaka da jamhuriyar Nijar.

Talla

Kungiyar ta IS ta kuma dauki alhakin kashe sojan Faransa daya, da ya rasa ransa a lokacin da mayakan suka tarwatsa wata nakiya da suka binne, a dai dai lokacin motocin sulken Faransawan ke sintiri a yankin na Indelimane, kan hanyarsu ta zuwa Gao.

A Juma’ar da ta gabata, mayakan na IS suka kaiwa sansanin sojin na Mali dake Indlemiane farmakin, inda suka halaka adadin nasu da dama da kuma jikkata wasu 3, kwana guda bayan hakan kuma suka halaka sojan na Faransa mai mukamin Kofur, Ronan Pointeau mai shekaru 24.

A karshen watan Oktoban da ya wuce wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne, sun sace malamai 6 a yankin tsakiya Mali, saboda yin magana da kuma koyar da dalibai cikin harshen Faransanci.

Harin kuma ya zo ne bayan da wata kididdiga ta nuna cewar, sama da makarantu 900 aka rufe a sassan kasar Mali, sama da kashi 2 bisa 3 daga cikinsu kuma a yankin tsakiyar kasar na Mopti, saboda matsalolin tsaron da suka hada da na ta’addanci da kuma rikicin kabilanci.

A wani labarin kuma a farkon Oktoban da ya gabata Amurka ta dauki alkawarin biyan ladan dala miliyan 5, ga duk wanda ya taimaka mata da bayanai kan shugaban reshen kungiyar IS a yankin saharar Afrika, da yayi ikirarin kashe dakarun Amurkan da na Jamhuriyar Nijar shekaru 2 da suka gabata.

Amurka ta kaddamar da farautar Adnan Abu Walid al-Sahrawi ne bayanda ya dauki alhakin farmakin da mayakan IS suka kaiwa dakarun hadakar Amurka da Nijar a kauyen Tongo Tongo, ranar 4 ga watan Oktoban 2017, inda suka halaka sojin Amurka 4 da na Nijar 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI