kassoum Abdourahman mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, kan yawaitan hare-hare a yankin Sahel

Sauti 03:42
Dakarun tsaron Mali na sintiri a yankin Meneka na kasar
Dakarun tsaron Mali na sintiri a yankin Meneka na kasar Agnes COUDURIER / AFP

An ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku, daga Litinin din nan a kasar Mali, don nuna juyayin kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa sojojin kasar 50 a karshen makon da ya gabata.Kafin wannan hari na kasar Mali, an samu faruwar makamancinsa a jamhuriyar Nijar, inda suka aka hallaka sojojin kasar 12, lamarin da ya sa ake diga ayar tambaya dangane da amfani ko rashin amfanin dubban dakarun kasashen Yammacin Dunia cikin wadannan kasashe na yankin Sahel.Dangane da wannan batu, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alkassoum Abdourahman mai sharhi kan lamurran yau da kullum, ga kuma zantawarsu.