Ministan tsaron Faransa na ziyarar aiki a Chadi

Ministan tsaron Faransa Florence Parly, yayin jawabi a Chelkwatan tsaron kasar dake birnin Paris ranar 10, ga watan Oktoban 2019
Ministan tsaron Faransa Florence Parly, yayin jawabi a Chelkwatan tsaron kasar dake birnin Paris ranar 10, ga watan Oktoban 2019 REUTERS/Benoit Tessier

Ministar ma’aikatar tsaron Faransa Florence Parly na gudanar da ziyara a kasashen yankin Sahel, a daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da kashe sojoji a Mali da Burkina Faso da kuma jamhuriyar Nijar.A zangon farko na wannan ziyara, minista Parly ta ce za a dauki dogon lokaci kafin a murkushe ayyukan ta’addanci a yankin na Sahel.

Talla

A cewar ta "Wannan yaki ne da tuni muka sani cewa zai dauki dogon lokaci, sannan kuma yana da matukar wuya, muna neman hadin kan kasashe irinsu Chadi saboda muhimmancinsu a wannan tafiya. Na samu damar tattaunawa da takwarorinmu na rundunar G5-Sahel domin yin dubi a game da irin ci gaban da aka samu".

Uwargida Parly ta bada misali da ce:

"Idan ku ka dauki misali, a bangaren arewa na yankin Sahel, kwanakin da suka gabata mun kai samamen hadin gwiwa inda muka yi nasarar ganowa tare da kwace tarin makamai, wannan daya ne daga cikin nasararin da muka samu".

Florence Parly ta bayyana muhimmacin aiki tare da kasashen Afirka wajen yaki da ta'addanci:

"A ganawarmu da shugaba Idris Deby, na bayyana masa muhimmancin ci gaba da yin aiki a tare a daidai wannan lokaci da rundunar G5-Sshel ke daf da fara aiki gadan-gadan karkashin jagorancin babban kwamandata Janar Namata".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.