Najeriya ta gindaya sabbin sharidodi kafin bude iyakokinta

Wani sabon ra'uran a shingen binciken kan iya tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin,domin tantance masu shiga kasar da Najeriya ta tanadar
Wani sabon ra'uran a shingen binciken kan iya tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin,domin tantance masu shiga kasar da Najeriya ta tanadar REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sharidodin da take bukatar ganin an aiwatar da su kafin ta bude iyakokin ta,Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyama ya bayyana haka, bayan wani taro da suka gudanar a Abuja.

Talla

Sharidodin sun hada da cewar, duk wani kaya da ake bukatar shiga da shi Najeriya daga kasashen ECOWAS, dole ya kasance yadda yake daga kasar da ya fito, ba tare da bude shi ba, kuma wajibi ne a raka shi har iyakar Najeriya.

Sharidodin sun kuma bukaci kayayyakin da ake fitarwa daga kasashen ECOWAS su cika dokokin kungiyar, yayin da masu fitowa daga wajen yankin kuma zasu biya sama da kashi 30 na kudin fito.

Najeriya ta kuma bukaci rusa manyan gidajen aje kayayyakin dake iyakokin kasashen dake makotaka da ita.

Kasar ta kuma bukaci sarrafa kayayyakin kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Najeriya tace ya zama wajibi mutanen dake zirga zirga kan iyakokin su kasance masu dauke da takardun shaida.

Ana saran wakilan kasashen Najeriya da Nijar da Jamhuriyar Benin su gudanar da wani taro nan da makwanni biyu domin nazarin sharidodin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI