Sojojin Masar sun hallaka 'yan ta'adda 83 a yankin Sinai

Dakarun tsaron Masar a yankin Sinai na kasar
Dakarun tsaron Masar a yankin Sinai na kasar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Dakarun Kasar Masar sun sanar da kashe ‘Yan tawaye 83 a Yankin Sinai dake fama da rikicin ‘yan ta’adda, Yankin da Kungiyar ISIS suka dade suna cin karen su babu babbaka.

Talla

Jami’an tsaro Masar sun sanar da hallaka yan ta’adda 77, bayanda aka kama su da tarin makamai a arewaci da tsakiyar yankin Sinai.

Har ila yau, sanarwar da dakarun suka fitar na cewa a wani gagarumin farmaki na kasa domin kakkabe ‘yan ta’adda, wanda ya auku a tsakanin ranar 28 na watan Satumba zuwa ranar 4 ga watan Oktoban nan da muke ciki, Wasu tantiran yan tawaye 6 sun gamu da ajalinsu a yankin, yayin da wasu dakaru 3 suka jikkata.

Sanarwar ta ce a halin yanzu dai an kame mutane masu laifi 61, daga cikin su akwai wadanda aka shafe lokaci ana nema.

A farmakin da dakarun suka kai domin kakkabe ‘yan ta’addan, sun yi nasarar lalata sansanoni da kuma motocin mayakan da dama.

Kididdigar baya-bayan nan da jami’an tsaron suka fitar na nuna adadin ‘yan ta’addan da aka kashe a yankin Sinai ya haura 830.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.