Bakonmu a Yau

An bude taron kasa da kasa kan tsaron Afrika a Dubai

Sauti 03:24
Janar Sani Usman Kukasheka da sauran masu halartar taron tsaro na kasa da kasa a Dubai.
Janar Sani Usman Kukasheka da sauran masu halartar taron tsaro na kasa da kasa a Dubai. RFI/Hausa

An bude taron kasa-da-kasa na kwanaki biyu kan inganta harkokin tsaron nahiyar Afirka a birnin Dubai na Hadeddiyar Daular Larabawa.Taron karo na 16 wadda kungiyar dake sa’ido kan rikice-rikicen Afirka wato Africa Security Watch ke shirya wa, kan gayyato jami’an gwamnati da shugabannin tsaron kasashe, da masana harkokin tsaro daga kasashe daban – daban, domin Nazari kan matsalolin tsaro da nahiyar ke fuskanta domin magance su.Kazalika Taron na zakulo wadanda sukayi fice wajen bada gudunmuwa kan harkokin tsaron kasashensu daga jami’an tsaro da fararen hula don basu kyaututtuka da lambobin yabo.Dangane da wannan taro Ahmad Abba ya tattauna da Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka wanda ke daya daga cikin masu halartan wannan taron, ga kuma yadda zantawarsu ta kasance.