Sudan ta Kudu

Machar da Kiir sun tsawaita wa'adin gwamnatin hadaka

Salva Kiir da Riek Machar
Salva Kiir da Riek Machar YONAS TADESSE / AFP

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da jagoran adawa na kasar Reik Machar sun amince da wa’adin karin kwanaki 100 nan gaba don samar da gwamnatin hadaka bayan da suka gaza sasantawa na tsawon lokaci don samar da dawwamammiyar zaman lafiya a kasar.

Talla

Tun a shekara ta 2013 ne mutanen biyu suka raba gari bayan da Machar da ke zama mataimakin Salva Kiir ya balle, sannan magoya bayansu suka yi ta fada da juna, lamarin da ya haddasa salwantar dubban rayukan mutane.

Wannan karin wa'adi na kwanaki 100 ya biyo bayan zaman da aka gudanar  karkashin inuwar wasu kasashen da ke kusa da s, a kasar Uganda.

Sau biyu ana zakudawa da wa'adin da ake diba masu, bayan da suka sanya hannu cikin yarjejeniyar fahimtar juna a watan Satumba, wanda hakan ne yasa suka jingine yakin da suke fafatawa.

Bangarorin biyu sun amince da samar da gwamnatin hadin-kai zuwa 12 ga wannan wata da muke ciki, amma kuma yanzu haka da wa'adin ya zakudo ne kuma, suka sake shawara na kara zakudawa da wa'adin zuwa nan da kwanaki 100 don samar da gwamnatin hadin kai.

Ministan Wajen Uganda Sam Kutesa ya fada wa manema labarai bayan zama da bangarorin biyu, cewa hakkun za su sa idanu don ganin an kai ga nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI