kamaru

Yara da dama na bukatar agaji a Kamaru - UNICEF

Shelkwatar UNICEF a Geneva.
Shelkwatar UNICEF a Geneva. REUTERS/Denis Balibouse

Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta sanar da cewa akalla mutane miliyan 1 da dubu dari 9 ne ke bukatar taimakon agaji a yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin Kamaru, wadanda daga cikin su rabi kananan yara ne.

Talla

A jawabin da Kakakin hukumar Marixie Mercado ta gabatar wa majalisar a birnin Geneva na kasar Switzerland, ta ce matsalar jinkai na ci gaba da karuwa ganin yadda ta shafi mutane kusan miliyan 2, adadin da ya karu sau 15 tun daga shekarar 2017.

UNICEF ta ce matsalar ta yi sanadiyar hanawa kananan yara samun ilimi, ganin yadda dubban makarantu suka kasance a rufe sakamakon hare haren ‘yan aware masu neman cin gashin kansu.

Mercado ta ce sama da yara dubu 855 ne suka fice daga makaranta sakamakon rikice rikicen yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar ta kamaru.

Shi kuwa kakakin hukumar bayar da agaji ta majalisar dinkin duniya OCHA, Jens Laerke ya bayyana cewa an yi garkuwa da yara mata ‘yan makaranta 3 a cikin watan da ya gabata, sannan yace rashin samun tallafi ne matsalar da ta addabi kasar kamaru ganin cewa kashi 41 cikin 100 na dala miliyan 299 da ta bukata ne ta samu.

Laerke ya ce matsalar lalatattun hanyoyi da ta shafi kashi 65 na wadannan yankuna, ya hana wa ma’aikatan agaji gudanar da ayukansu saboda fargabar kada a yi garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI