Burkina Faso

Ana alhinin rasuwar mutane 37 a Burkina Faso

Shufgaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré, 28-11-2017.
Shufgaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré, 28-11-2017. LUDOVIC MARIN / POOL / AFP

Ana zaman makoki na tsawon kwanaki uku a Burkina Faso, bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane 38 da ke aiki da wata mahakar zinari da ake kira Semafo a yankin gabashin kasar ranar larabar da ta gabata.

Talla

Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ne ya sanar da ware kwanaki uku bayan wani taron gaggawa da ya hada manyan kusoshin gwamnati da na tsaro a birnin Ouagadougou.

Ranar laraba da ta gabata ne gwamnan lardin Gabashinkasaar Saidou Sanou, ya sanar da cewa ‘yan bindiga sun kai harin kwonton bauna kan ayarin ma’aikatan mahakar zinari ta Semafo, inda suka kashe mutane 37 yayin da wasu akalla 60 suka samu raunuka.

Bayanai sun ce da farko motar jami’an tsaron da ke yi wa fararen hular rakiya ce ta taka nakiya, daga nan kuma sai ‘yan bindigar suka bude wuta a kan motar da ke dauke da ma’aikatan kamfanin.

Majiyoyi sun ce yanzu haka ana ci gaba da neman wasu mutane da suka bata lokacin harin, yayin da ake dangane da lamarin da mayaka masu ikirarin jihadi da suka jima suna kai farmaki a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.