Congo

An daure madugun'yan tawayen Congo Bosco Ntaganda shekaru 30

Bosco Ntaganda ranar 28 ga watan agustan 2018 gaban Kotun  Duniya da ke Hague
Bosco Ntaganda ranar 28 ga watan agustan 2018 gaban Kotun Duniya da ke Hague Bas Czerwinski / ANP / AFP

Kotun hukunta manyan laifuffuka a duniya ta yanke wa tsohon madugun ‘yan tawayen Jamhuriyar Congo da Bosco Ntaganda hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari sabioda samun shi da aikata laifufukan yaki.

Talla

Wannan hukunci shi ne mafi tsanani da kotun ta taba yanke wa mdugun wata kungiya ta ‘yan tawayen a tarihi.

An sami Ntaganda da aikata laifuka da dama ciki har da kasha-kashe, bautar da jama’a, shigar da kanana yara a aikin soji a yankin Ituri mai arzikin ma’adinan. Har ila yau an samu Ntaganda da ake kira da suna Ternimator da laifin cin zarafin mata tare da galaza wa fararen hula.

Da dama daga cikin laifukan da aka tuhumi tsohon madugun ‘yan tawayen mai shekaru 46 da aikatawa, na da alaka da kisan gillar da aka yi wa mazauna wasu kauyuka, a matsayinsa na mai bayar da umurni ga dakarunsu.

A cewar kungiyoyin kare hakkin dan adam, sama da mutane dubu 60 ne aka kashe daga lokacin da rikici ya barke a yankin Ituri a shekarar 1999,

Kakakin babbar kotun ya bayyana hukuncin a matsayin mafi tsanani da aka taba yanke wa masu aikata manyan laifuka tun kafuwar kotun a shekarar 2002.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.