Afrika

Mutane milyan 530 zasu fuskanci karancin hasken wutar lantarki a 2030

Matsalar samar da hasken wutar lantarki  a Afrika
Matsalar samar da hasken wutar lantarki a Afrika DESMOND KWANDE / AFP

Sama da mutane milyan 530 zasu fuskanci barazanar karancin hasken wutar lantarki a shekara ta 2030, rahoton da hukumar dake kula da makamashi ta fitar a yau juma’a na nuna ta yada gwamnatocin Afrika suka kasa cika gibin da ake fuskanta yanzu haka dangane da zantukan da suka jibanci makamashin hasken wutar lantarki a kasashen su.

Talla

Wasu kasashen dake sayar da wutar lantarki zuwa wasu kasashen sun kasa wadatar da al’umar su da wannan makamashi bisa wasu dalilai can daban.

A afrika kasashe da suka hada da Ghana,Najeriya na daga cikin masu sayar da wutar zuwa kasashen Nijar, Benin, Cote D’Ivoire.

A wannan rahoto da hukumar ta fitar a yau akala mutane milyan 600 a nahiyar Afrika suke bukatar hasken wutar lantarki, yayinda manyan kamfanoni a Nahiyar ba su wadata da isashen hasken wutar lantarki cikin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.