Najeriya-Benin

Patrice Talon na Benin ya damu da rufe iyakar kasar da Najeriya

Shugaban Benin, Patrice Talon rna zantawar da Christophe Boisbouvier (RFI) da Marc Pereleman (France 24).
Shugaban Benin, Patrice Talon rna zantawar da Christophe Boisbouvier (RFI) da Marc Pereleman (France 24). RFI/France24

Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon, wanda ke zantawa da tashar talabijin ta France 24 da kuma RFI, ya ce tsohon shugaban kasar Bony Yayi na iya komawa kasar saboda tuni aka yi wa wadanda ke da hannu a tarzomar da aka yi bayan zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar bana.

Talla

Hakazalika a wannan tattaunawa Talon, ya ce ya damu matuka a game da matakin rufe iyaka da mahukuntan Najeriya suka dauka yau kusan watanni uku, lamarin da ya shafi alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A wani bangare na tattaunawar da France 24 da kuma RFI, shugaba Patrice Talon ya ce nan ba da jimawa ba, ‘’kasashen Afirka da ke amfani da takardar kudin CFA gungun BCEAO, za su dauki matakin janye kudaden ajiyarsu da ke baitul malin Faransa’’, wanda shi ne matakin farko na janyewar kasashen daga CFA.

Shugaban na Jamhuriyar Benin ya ce shugabannin kasashe mambobi a UEMOA da kuma shguaba Emmanuel Macron, dukkaninsu sun amince da sauye-sauyen da ake yi game da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI