Guinea Bissau

ECOWAS ta tilastawa Fira Minista yin murabus

Sabon Fira Ministan Guinea Bissau Faustino Fudut Imbali yayi murabus, bayan da kungiyar hadin kan kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta bashi wa’adin yin hakan.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, tare da wasu shugabannin kasashen ECOWAS, yayin taro na musamman kan rikicin siyasar Guinea Bissau a birnin Yamai
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, tare da wasu shugabannin kasashen ECOWAS, yayin taro na musamman kan rikicin siyasar Guinea Bissau a birnin Yamai Africanews
Talla

A mako jiya shugaban Guinea Bissau Jose Mario Vaz ya bayyana Imbali a matsayin sabon Fira Minista, to sai dai tsohon Fira Ministan ta ya kora Aristides Gomes ya yi tsayuwar gwamen jaki kan kin amincewa da matakin, abinda ya haifar da rikicin siyasa a kasar.

Wannan tasa shugaba Vaz rushe gwamnatin da sake kafa sabuwa, matakin da kungiyar ECOWAS ta ce ba za amince da shi ba, yayin taron musamman da ta yi kan rikicin siyasar kasar ta Guinea Bissau jiya Juma’a a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Yayin taron ne kuma, ECOWAS ta baiwa sabon Fira Minista Imbali wa’adin yin murabus, ko kuma ta kakabawa Guinea-Bissau takunkuman karya tattalin arziki.

Ranar 24 ga watan Nuwamban nan na 2019, za a gudanar da zaben shugabancin kasar ta Guinea Bissau, wanda shugaba mai ci ke neman karin wa’adi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI