Afrika

Yan sanda sun ceto mutane 64 daga masu safarar mutane a Mali

Wasu daga cikin matan da aka ceto daga hannun masu safarar mutane
Wasu daga cikin matan da aka ceto daga hannun masu safarar mutane PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Hadin gwiwar ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol da takwarorinsu na Mali sun ceto mutane 64 mafi akasarinsu mata manya da kanana daga masu safarar mutane dake bautar da su.

Talla

‘Yan sandan na Interpol sun ce an yo safarar wadanda aka ceton ne zuwa birnin Bamako, daga kasashen, Najeriya, Burkina Faso, da kuma kasar ta Mali, inda ake tilasta musu karuwanci, bauta da kuma bara, a mashaya, gidaje da kuma wuraren hakar ma’adanai.

Tuni dai jami’an tsaron suka damke mutane wasu mutane 4 da ake zargi da safarar mutanen, yayinda aka baza komar kamo wadanda suka tsere.

Wani rahoton hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM, yace sama da ‘yan ci rani dubu 160 ne suka shiga Mali ko aka yi safararsu, tsakanin watan Yulin 2016 zuwa karshen watan Janairun shekarar 2019.

Mali dai na daga cikin cibiyoyin da ‘yan ci rani ke bi domin nahiyar Turai, to sai dai a lokuta da dama, masu safarar mutane kan yi amfani da damar wajen bautar da su, da kuma tilastawa mata manya da kanana karuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI