Gambia-Myanmar

Gambia ta shigar da karar Myanmar gaban kotun Duniya

Wasu daga cikin dubban 'yan kabilar Rohigya Musulmi akan hanyar tsallakawa Bangladesh bayan tserewa daga Myanmar. 19/10/2017.
Wasu daga cikin dubban 'yan kabilar Rohigya Musulmi akan hanyar tsallakawa Bangladesh bayan tserewa daga Myanmar. 19/10/2017. ©REUTERS/Jorge Silva

Kasar Gambia ta shigar da kara kotun duniya inda take zargin gwamnatin Myanmar da aikata laifuffukan yaki da cin zarafin dan adam ta hanyar kisan gilla ga Musulmi Yan kabilar Rohingya tsiraru dake kasar.

Talla

Ministan shari’ar Gambia, Abubacar Tambadou ya shaidawa manema labarai cewar sun gabatar da karar a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da suka amince da halarcin kotun ta duniya tare da Myanmar.

Ministan yace matakin wata dama ce da za ta baiwa Myanmar damar amsa laifin ta, wadda ta bayyana a matsayin abin kunya da ba za’a amince da shi a irin wannan lokaci ba.

Tuni dai kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta tubewa jagorar gwamnatin kasar ta Myanmar Aung San Suu kyi lambar girma mafi daukaka da ta ba ta, saboda yadda ta kauda kai lokacin da sojojin kasar ke cin zarafin Musulmi 'yan kabilar Rohingya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.