Najeriya-Ghana

GUTA za ta durkusar da harkokin 'yan Najeriya a Ghana

Wasu daga cikin mambobin kungiyar kwadago ta Ghana
Wasu daga cikin mambobin kungiyar kwadago ta Ghana Daily Trust

Kungiyar Kwadagon Ghana GUTA na shirin gudanar da gagarumin aikin rufe shagunan ‘yan Najeriya da ke birnin Accra, matakin da ake kallo a matsayin ramuwar gayya kan rufe iyakokin Najeriya.

Talla

Kawo yanzu Kungiyar Kwadagon ta GUTA ta rufe shagunan ‘yan Najeriya kimanin 70 da zummar durkusar da harkokin kasuwancin ‘yan Najeriyar a birnin Accra.

Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya da ke Ghana, Chukwuemeka Nnaji ya bukaci mambobin kungiyar da su rufe shagunansu domin kauce wa fashe-fashe ko kuma lalata musu kayayyakinsu na sana’a.

Kiris ya rage a yi mummunar arangama tsakanin ‘yan Ghana da ‘yan Najeriya a jiya a birnin na Accra saboda yadda kungiyar kwadagon ke ci gaba da rufe shagunan.

Matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na rufe kan iyakokinta da kasashe makwabta da suka hada da Ghana, ya jefa harkokin ‘yan kasuwan na Ghana cikin wani hali.

Najeriya ta jaddada cewa, ba za ta bude kan iyakarta a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI