G5 Sahel

Guterres da Macron sun bukaci karfafa runudunar G5 Sahel

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron. Reuters/Benoît Tessier

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun bukaci kara taimakawa rundunar G-5 Sahel dake yaki da Yan ta’adda a Yankin Afirka ta Yamma.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar nan bada makwanni masu zuwa zasu dauki matakin taimakawa rundunar ta G-5 Sahel wadda ke kokarin murkushe Yan ta’addar da suke yiwa Yankin Sahel barazana.

Macron wanda ya fadi haka lokacin da ya karbi tawagar shugabannin kasashen Chadi da Nijar da kuma Mali da suka ziyarce shi a fadar Elysee, yace sun samu cigaba a matakan soji da suke dauka, kuma zasu dada karfafa rawar da dakarun Barkhane ke takawa domin samar da tsaro a Yankin.

Shugaban yace kuma zai janyo hankalin kasashe kawayen Faransa da suka yi alkawarin taimakawa rundunar amma kuma ake cigaba da fuskantar jinkiri.

Rahotanni sun ce shugaba Macron da Idris Deby da Mahamadou Issofou da Ibrahim Boubacar Keita sun kuma tattauna halin da ake ciki a kidal.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwa kan harkokin tsaron Yankindake cigaba da tabarbarewa, yayin da ake cigaba da asarar dimbin rayuka.

Guterres ya bukaci kara taimako ga dakarun dake aiki a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI