Cameroon- France

Wasu 'yan kasar Kamaru sun yi zanga-zanga a Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.

Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru
Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru RFI

Darururwan 'yan kasar Kamaru ne mazauna birnin Paris suka kutsa kai cikin wani Otel da aka sauke Shugaban kasar Kamaru Paul Biya da matarsa Shantal don yin zanga-zanga saboda halin da kasar tasu ke ciki. 

Talla

Masu zanga-zangan sun rika bayyana halin da kasar Kamaru take ciki da cewa babu kyau, yadda ake tafiyar da Gwamnati.

Shugaba Paul Biya na birnin Paris ne don halartan taro da takwaransa Emmanuel Macron ya kira shugabannin kasashen duniya don tattauna batun zaman lafiya a duniya.

Wannan taro a Paris ya sami halarci shugabannin kasashen duniya da dama inda suka tattauna batutuwa da dama a jere na kwanaki biyu, Talata da Labara.

Uba Danlami Sarkin Hausawan 'yan kasar Kamaru mazauna Turai ya bayyana cewa wasu daga cikin bukatun masu boren na da kanshin gaskiya yayin da wasu bukatun babu.

Sai dai kuma ya bayyana cewa zanga-zangan da aka yi basa goyon bayan haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI