Kamaru

Jam'iyyar SDF ta lashe amanta kan zabukan watan fabarairu

Joshua Osih, mataimakin shugaban jam'iyyar adawa ta Social Democratic Front (SDF) a Kamaru.
Joshua Osih, mataimakin shugaban jam'iyyar adawa ta Social Democratic Front (SDF) a Kamaru. osih.com

Jami’iyyar adawa ta biyu mafi karfi a Kamaru SDF, tayi amai ta lashe kan zaben kananan hukumomi da na ‘yan majalisa, wanda a baya ta sha alwashin kauracewa.

Talla

Jami’yyar dake karkashin jagorancin John Fru Ndi, ta sha alawashin kauracewa zabukan ne, saboda tashe-tashen hankulan da yankunan masu amfani da turancin Ingilishi a arewa maso yammci da kuma kudu maso yammacin Kamaru ke ciki.

Sai dai bayan tuntubar juna bisa jagorancin mataimakin shugabanta Joshua Osih, jam’iyyar ta SDF a yanzu ta ce shiga zabukan yana da muhimmanci, sai dai hakan ba ya nufin za ta sassauta kan gaggauta kawo karshen tashe-tashen hankula a yankunan dake amfani da turancin ingilishi, kafin zaben kananan hukumomin ya gudana a ranar 9 ga watan Fabarairu na shekarar 2020 dake tafe.

Jam’iyyar adawar ta SDF, ta kuma yi gargadin cewa muddin zuwa tsakiyar watan Disamba mai zuwa, gwamnatin Kamaru ta gaza daukar matakan maido da zaman lafiya a yankunan ‘yan awaren, ko aiwatar da shawarwarin da taron zaman lafiyar kasar na cikin watan Satumban da ya gabata ya bayar, to fa za ta koma kan tsohon alwashin da ta sha, na kauracewa zabukan dake tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI