Najeriya

Hukumar INEC ta gano ma'aikatan da aka sace a zaben Kogi

Ma'aikatan hukamar zaben Najeriya ta INEC
Ma'aikatan hukamar zaben Najeriya ta INEC REUTERS/Tife Owolabi

Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da gano ma’aikatan 30 da ta bayyaan cewar sun bace, sakamakon tashin hankalin da aka samu lokacin gudanar da zaben Gwamnan Jihar Kogi jiya asabar.

Talla

Kakakin hukumar, Rotimi Oyekanmi ya sanar da cewar an gano ma’aikatan da aka tura karamar hukumar Olamaboro kuma yanzu haka suna cikin koshin lafiya.

Oyekanmi yace shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu yayi Magana da wasu daga cikin su, kuma sun tabbatar da halin da suke ciki.

Mutane na cikin dakon sakamakon zabe, yayinda kungiyoyi masu zaman kan su ke ci gaba da yin kira ga al’uma na su kaucewa tada zaune tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.