Burkina Faso

Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda

Wasu sojojin Burkina Faso
Wasu sojojin Burkina Faso AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO

Sojojin Burkina Faso sun yi nasarar kashe mayakan jihadi 32 a lokacin da suka yi kokarin kaiwa dakarun kasar hari daf da garin Yorsala dake lardin Loroum a wani daji dake yankin.

Talla

A wannan gumurzu sojan Burkina Faso daya ne ya rasa ran sa, sojojin Burkina faso sun samu nasarar kwace makaman yaki daga hannun mayakan jihadi.

Mata da dama dai ne sojojin Burkina Faso suka ‘yanto daga hannun yan jihadi.

Maharan jihadi na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan kasar ta Burkina Faso tareda kisan sojoji da fararren hula.

Lamarin ya sa da dama daga cikin mazauna kauyukan kasar tserewa daga gidajen su a dan tsakanin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI