Senegal

Kasashen duniya na taro kan tsaro a Afrika

Akwai bukatar karfafa dakarun da ke yaki da ta'addanci a Sahel
Akwai bukatar karfafa dakarun da ke yaki da ta'addanci a Sahel Michele Cattani/AFP/Getty Images

A daidai lokacin da aka bude taron kasa da kasa kan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afrika, shugabannin kasashen Senegal da Mauritania sun bukaci karfafa dakarun da ke yaki da mayakan jihadi a yankin Sahel.

Talla

Shugaban Senegal, Macky Sall da ke karbar bakwacin taron a birnin Dakar ya ce, akwai kimanin dakaru dubu 30 da suka hadada na Mali da kasashen Turai a lardunan da a yaznu haka ke hannun wani gungun na ‘yan bindiga, yana mai cewa, wannan gagarumar matsala ce, yayin da ya diga ayar tambaya kan abinda ke hana magance wanann matsalar.

Sall ya kuma bukaci kasashen China da Rasha da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da su goyi bayan karfafa rundunar Minusma a kasar Mali, yayin da ya gargadi cewa, yin sakaci ka iya haddasa kwararowar mayakan jihadin da aka ci galabar su a Iraqi da Syria cikin Afrika.

Shi ma shugaban Mauritani, Mohamed Cheil Ould el-Ghozouni ya ce, dole Majalisar Dinkin Duniya ta samar da sauye-sauye a tsare-tasrenta na tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel.

El-Ghozouni ya ce, akwai bukatar kwararrun dakarun sintiri na Sahel su rika samu cikakken damar aiwatar da ayyukansu a maimakon jibge su a wuri guda, yana mai cewa, dole Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da karin tallafin kudade ga rundunar G5 Sahel wadda kawo yanzau ba a ba ta kayyakin da alkawaranta mata ba.

Taron na birnin Dakar, na samun halartar kwararru kan sha’anin tsaro da jami’an gwamnatocin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI