Burkina Faso

Burkina Faso: Tilas Faransa ta nemi izini kafin mamayar 'yan ta'adda

Daya daga cikin jiragen yakin Faransa na rundunar Barkhane dake yakar ta'addanci a yankin Sahel.
Daya daga cikin jiragen yakin Faransa na rundunar Barkhane dake yakar ta'addanci a yankin Sahel. Image: État-major des armées

Burkina Faso ta bukaci Faransa, wadda ta girke sojojinta dake yaki da ‘yan ta’adda a Yankin Sahel, da ta rika sanar da ita kafin yin amfani da jiragen yaki, wajen kai farmaki kan mayakan masu ikirarin jihadi.

Talla

Wata wasika da rundunar sojin ta Burkina Faso ta rubutawa Jakadan Faransa, dauke da sanya hannun Janar Moise Minidou, ta bukaci Faransar ta rika sanar da ita kafin kai farmaki da akalla sa’oi 48.

Jami’in yace sun sanar da rundunoninsu cewar daga yanzu, muddin basu samu irin wannan sanarwar ba, zasu dauki duk jiragen yakin da suka gani suna shawagi a matsayin na abokan gaba.

A baya bayan nan dai hare-haren 'yan ta'adda sun karu a kasashen dake yankin Sahel musamman Burkina Faso, inda a farkon watan Nuwamba, 'yan ta'addan suka kai wani mummunan hari a kasar,inda suka kashe jami'an tsaro biyar, harin da ke zuwa a daidai lokacin da ake zaman makoki a Mali biyo bayan kisan da 'yan ta'ddan suka yi wa sojojin kasar kimanin 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI