Mali

Mali ta rasa dakaru 24 yayin gumurzu da 'yan ta'adda

Wasu sojojin kasar Mali.
Wasu sojojin kasar Mali. AFP/Marco LONGARI

Rundunar Sojin kasar Mali tace Yan ta’adda sun kashe mata dakaru 24 a fafatawar da suka yi a Gabashin kasar, yayin da su kuma suka kasha 17 daga cikin su.

Talla

Sanarwar rundunar sojin ta Mali dake nuna ci gaba da tabarbarewar tsaro a kasar, tace bayan sojoji 24 da suka mutu a gwabzawa da ‘yan ta’addan, wasu dakarun 29 sun jikkata, yayinda su kuma, suka kashe 17 daga mayakan, gami da kame wasu sama da 100.

Sanarwar tace sojin sun kaddamar da hari ne kan mayakan tare da sojin Jamhuriyar Nijar, bayanda Yan ta’addan suka kai musu hari a Tabankort.

Sanarwar sojin Mali tace sojojin Nijar da na Faransa sun taka rawa wajen fafatawar da akayi, kuma yanzu haka wadanda aka kama daga cikin Yan ta’adda na tsare a hannun sojin Nijar.

Wannan karawa ba karamar koma baya bace ga sojin Mali wadda tayi asarar sojoji sama da 100 a wata guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI