Ba yau na saba taimaka wa marasa galihu ba- Adam Zango

Tauraron dan wasan Hausa kuma mawaki Adam A Zango tare da Ahmed Abba na RFI
Tauraron dan wasan Hausa kuma mawaki Adam A Zango tare da Ahmed Abba na RFI RFI/Ahmed Abba

Tauraron shirya fina-finan Hausa, kuma mawaki Adam A Zango ya tabbatar da biyan kudin karatun wasu dalibai na shekaru uku, inda ya kashe fiye da naira miliyan 46.Tun bayan da Mawakin ya wallafa takardar tabbatar da samun tallafin da ta fito daga makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke Zaria, na daukar nauyin karatun yara 101, wadanda yawancin su marayu ne da kuma yaran da suka fito daga gidajen marasa galihu a shafinsa na Instagram, aka shiga cece-kukce a ciki da wajen kasar.Ahmed Abba ya samu tattaunawa da Fitaccen jarumin Adam A. Zango, da yanzu haka ke ziyara a birnin Lagos, Ya kuma bayyana dalilin fitarsa daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ga yadda zantawar ta gudana.

Talla

Ba yau na saba taimaka wa marasa galihu ba- Adam Zango

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI