Adadin mutanen da ke mutuwa sakamokon nakiyoyin da aka binne ya karu a Duniya

Dakarun Koriya ta arewa na neman nakiyoyi da aka binne karkashin kasa
Dakarun Koriya ta arewa na neman nakiyoyi da aka binne karkashin kasa Song Kyung-Seok/Pool via REUTERS

Wani sabon rahoto ya nuna yadda aka samu karuwar asarar rayuka ko samun raunuka a Duniya, sakamakon yadda ‘yan bindiga ke amfani da abubuwan masu fashewa da suke kerawa da kansu.

Talla

Rahoton yace cikin shekara daya kachal, Kimanin mutane dubu 3,800 aka kashe ko raunata su a bara kadai ta wannan hanyar, adadi mafi yawa da aka taba gani a baya.

Rohotan da kungiyar da ke sa ido kan Yarjejeniyar haramta amfani da nakiyoyi da ake binnewa a karkashin kasa, tace lamarin na barazana ga yarjejeniyar hana amfani da makaman na fiye da shekaru 20.

Rohotan yace, tun bayan yarjejeniyar a shekarar 1999, adadin wadanda ke mutuwa ko samu rauni, sakamakon abubuwa masu fashewa ya ragu ainun daga kussan dubu 10, zuwa kasa da dubu 3 da 500 a shekarar 2013.

Stephen Goose, shugaban sashin kula da rikicin makamai a kungiyar kare hakkin dan adam na Human Rights Watch, kuma mai ba da gudummawa ga kungiyar, yace, yarjejeniyar da kashe 164 suka kulla ta yi tasiri kwarai da gaske hatta ga kasashen da basa cikin yarjejeniyar.

Goose yace, Kasar Myanmar, wacce ba ta cikin yarjejeniyar, ita ce kasa daya tilo da sojojin gwamnati suka yi amfani da nakiyoyin a shekarar da ta gabata.

Sai dai fa, a yayin da kusan daukacin kasashen duniya ke kaucewa amfani da abubuwan masu fashewa, batun na kara ta’azzara a bangaren kungiyoyin da ke dauke da makamai.

Rohaton yace, a shekarar da ta gabata, irin wadannan kungiyoyi sun yi amfani da nakiyoyi kirar hannu, a kasashe akalla shida da suka hada da Afghanistan, da Indiya, da Myanmar, da Najeriya, da Pakistan da kuma Yemen, sai kuma kasashen da ba’a kai ga tabbatarwa ba, irin Kamaru da Kolombiya da Mali da Philippines da Somaliya sai Tunisiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.