Najeriya

Barayin mutane sun fara bi gida gida a Najeriya

Hoton da ke misalta 'yan bindigan da suka sace mutane a Kaduna.
Hoton da ke misalta 'yan bindigan da suka sace mutane a Kaduna. Jakarta Globe

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya na cewa wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun afka wa unguwar Hayin Dan Mani da ke karamar hukumar Igabi da sanyin safiyar Laraba, inda suka yi awon gaba da mutane shida, ciki har da wata mace mai shayarwa har ma da danta.

Talla

‘Yan bindigan sun shiga unguwar, kusa da Falwaya da karfe 3 da minti 15 na safe, kuma suka dinga harbin iska.

Sarkin Hayin Dan Mani Alhaji Abdullahi Abba wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce a  halin da ake ciki, ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan wadanda suka sace, inda suka bukaci a ba su naira miliyan 20 kan duk mutum guda.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigan sun kai 50, dauke da bindigogi, kuma gida – gida suka yi ta bi su na yi wa jama’a kamun – kazan – kuku.

Ba wannan ne karon farko da masu satar mutane suka bi mutane har gida suka kama ba a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya,saboda a kwanakin baya, wasu gungun 'yan bindiga sun addabi wasu ungwanni a jihar,inda suke wa mutane dauki - dai - dai.

Idan ba a manta ba, Ungwannin Nariya da Kakkau duk a jihar ta Kaduna sun taba yin kukan neman dauki sakamakon yadda masu satar mutane don neman kudin fansa suka addabe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI