Taron kasa-da-kasa kan canjin yanayi a kasar Ivory Cost

Injiya Mohammed Kabir Wanori da wasu masana a taron dumamar yanayi na kasar Ivory Cost
Injiya Mohammed Kabir Wanori da wasu masana a taron dumamar yanayi na kasar Ivory Cost RFI/Ahmed Abba

Masana harkokin yanayi da masu ruwa da tsaki daga nahiyar Afrika na gudanar da taro a birnin Abijan na kasar Cote d’Ivore, domin Nazari kan halin dumamar yanayi dake barazana ga Nahiyar dama duniya baki daya.

Talla

Taron kwanaki 2 wanda Bankin Duniya ya shirya, ya maida hankali kan yawaitar Ambaliyar ruwa a kasashen Afirka.

Shugabar Babban Bankin Duniya mai kula da wasu kasashen Afirka, Coralie Gevers tace, ruwan sama da akayi kamar da bakin kwarya da ta haifar da Ambaliya ta shafi mutane fiye da miliyan biyu a Afirka.

Eng. Kabiru Mohamed Wanori, kwamishinan Muhalli na Jahar Borno a Najeriya na daga cikin masu halartan taron, kuma yayi mana tsokaci.

Injiniya Kabir Wanori kan taron canjin yanayi a kasar Ivory Cost

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI