Yawancin 'yan yi wa kasa hidima a Najeriya sun kasa kare takardun shaidar su

RFI Convida
RFI Convida RFI

Shugaban Hukumar kula da ’yan yiwa kasa hidima da wadanda suka kammala karatun samun digiri a manyan makarantu na Najeriya, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim yace dalibai sama da dubu 16 da suka ce sun kammala karatun samun digiri a kasashen waje, sun kasa bayyana a gaban su domin kare takardun shaidar da suka samu.Janar Ibrahim yabce daga cikin irin wadannan dalibai 20,000 da suka gabatar da takardun su domin sanya su cikin masu zuwa bautar kasa, 3,240 kawai suka je suka kare takardun shaidar da suka samu, yayin da sauran suka yi batar dabo.Shugaban hukumar ya danganta wannan da takardun shaidar bogi da wasu bata garin ‘yan Najeriya ke zuwa suna sayowa a kasashen waje ba tare da sun yi karatun ba, inda ya bayyana jajircewar hukumar sa wajen ganin ta gano irin wadannan mutane domin hukunta su.Ga dai abinda ya shaida mana a tattaunawar su da Muhammed Sani Abubakar.

Talla

Yawancin 'yan yi wa kasa hidima a Najeriya sun kasa kare takardun shaidar su

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI