Turai

An kama wasu yan kasar Belgium a Cote D'Ivoire

Hukumar yan Sanda ta Turai Europol
Hukumar yan Sanda ta Turai Europol DR

Hukumomin kasar Belgium sun sanar da kama wasu mutane biyu da aka bayyana su cikin jerin mutanen da aka fi nema a Turai, saboda zargin kisan gillar da ake musu na kashe wani Dan kasar Birtaniya a shekarar 1996.

Talla

Tareda hadin gwiwar yan Sandar kasar Cote D’Ivoire da hukumar yan Sanda ta kasa da kasa ,Interpol ne aka samu nasarar cafke mutanen biyu a Abidjan.

An kama mutanen biyu Hilde Van Acker da Jean Claude Lacote ne a Abidjan dake Cote d’Ivoire bayan kwashe shekaru 20 ana neman su.

Ana zargin mutanen biyu ne da harbe Marcus John Mitchell a kai a gabar teku, inda daga bisani suka yi batar dabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.