Kamaru na fargabar CAF ta sake hana ta shirya gasa a 2021

Logon Hukumar Kwallon kafar Afirka CAF
Logon Hukumar Kwallon kafar Afirka CAF cafonline.com

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta ce, tana nazarin sauya lokacin da ya kamata ta gudanar da gasar kwallon kafar mai zuwa a bara da Kamaru zata karbi bakwanci.

Talla

Hakan ya fito fili ne a taron da kwamitin gudanarwar Hukumar ta gudanar jiya Alhamis a birnin Alkahira na kasar Masar, inda tace zatayi haka ne don dai-daita gasar da yanayin Afirka.

Cikin Sanarwar da hukumar CAF ta fitar,ta ce, za’a shirya gasar mai zuwa tsakanin watan Janairu da Afrelu maimakon Mayu zuwa Yuni da aka tsara tun farko, sabo da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake samu awasu kasashen Afrika, inji CAF, Inda tace, zasuyi nazarin sabon jadawalin tare da kasar da zata karbi bakwanci.

Lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan wasu masu shirhi dama hukumomin kwallon kafar kasar Kamaru da aka tsara zata karbi bakwanci.

Domin na farko zai kara masawa kasar Lamba cikin shirye-shiryen da takeyi da tunanin gasar zai gudana a tsakiyar shekarar 2021, sai gashin ana shirin dawo da lokacin baya zuwa kasa da watanni 6 kachal.

Na biyu kuwa shine yadda sanarwar kai tsaye ta kasa ambaton sunan kasar Kamaru a matsayin wanda za’ayi wannan shawara da ita, sai tace, kasar da zata karbi bakwanci, alhali kuwa a hukumance kasar ce, zata karbi bakwanci.

Hakan na jefa barazana ko hukumar CAF zata sake kwace damar da ta baiwa Kamaru mai rike da Kamabin na Afirka har 5, kamar yadda tayi a wanmnan farkon wannan shekara, inda ta mika gasar kasar Masar.

Don ko a ziyarda da tawagar kwararu ta hukumar ta kai Kamaru, ta tabbatar da cewa kasar bata kammala shirye-shiryen karban bakwancin gasar na 2021 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.